hijjartAbdoul
Rayuwa ba koyaushe take farawa da murmushi ba. Wasu kan taso ne cikin hawaye, rauni da tambayoyin da ba su da amsa. "Haske a Duhu" labari ne da ke bayyana irin wannan rayuwa, rayuwar da ta fara cikin duhu, amma ta ƙi yarda duhun ya cinye ta gaba ɗaya. Rashin uwa, wanda kowa ya sani uwa wata babbar jigo ce a cikin rayuwar mu, to ya abin zai kasance dan aka ce mutum ya tashi babu ita? Gefe ɗaya ya abin zai kasance idan aka ce ana takurawa mutum ya yi abinda be so ba? Akwai abubuwan da ke raunana zuciyar ɗan Adam, musamman matashi ko matashiya. Akwai ƙunci akwai kuma tsananin, ya akwai shariya gami da tausayi, amma duk da wannan abun, to wai ma meye ne zai kasance a sanda Me zai faru idan mutum ya taso ba tare da kulawar uba ba?
Me zai zama sakamakon muzgunawa daga wanda ya kamata ya zama garkuwa?
Ta yaya zuciya za ta iya sake amincewa bayan cin amana?
Kuma shin soyayya za ta iya zama haske a rayuwar da duhu ya mamaye?
"Haske a Duhu" labari ne mai cike da raɗaɗi, hawaye da gwagwarmaya, amma kuma cike da ƙarfi, bege da soyayya. Labarin ya nuna cewa ko a cikin mafi tsananin DUHU, akwai HASKE, haske na soyayya ta gaskiya, juriya, bege da ƙaddara.
Amma fa a sani ko bayan tsanin dare safiya tana zuwa.....